Baya ga masallacin Harami da ke Makkah, masallacin Annabi Muhammad SAW da ke birnin Madina shi ne mai daraja ta biyu, inda masallacin Baitil Muqaddis da ke Birnin Qudus ya zama mai daraja ta uku.